Wannan ya zama kari kan sunaye 28 da ya riga ya aika a makon da ya gabata.
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya gabatar da karin sunayen da ake bukatan tantancewa a matsayin Ministoci su 19 da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya aika wa Majalisar, a ciki har da wasu tsofaffin gwamnoni 5, da suka hada da Simon Lalong na Jihar Pilato, da Bello Matawalle na Jihar Zamfara, da Atiku Bagudu na Jihar Kebbi da Ibrahim Geidam na Jihar Yobe sai kuma Adegboyega Oyetola na Jihar Osun.
Wadanan sunaye sun kawo jimlar sunayen da aka mika wa majalisar zuwa 47 wanda yake nuna alamun za a kara yawan ma'áikatu. Yawan sunaye ya banbanta da na gwamnatocin baya da yawan su bai kai 47 ba.
Wannan ya jawo hankalin Jamiyyar Lebo inda mai magana da yawun ta Dokta Yunusa Tanko ya ce su ba su gamsu da wannan mataki ba, saboda yana ganin wadanda aka zabo su zama Ministoci ba a yaba da ayyukan da suka yi a baya ba. Yunusa ya ce Jamiyyar lebo tana ganin cewa ba bajinta aka yi ba saboda ya kamata a zakulo wadanda za su yi wa talakawa aiki ne, ganin mumunan halin yunwa da talauci da kasar ta ke ciki. Yunusa ya ce babu alamun tsofaffin gwamnoni da aka kawo sunayen su domin zama Ministocin za su yi wa kasa aikin gyara kamar yadda ya kamata.
Amma ga Sanata mai wakiltar Jigawa ta Arewa maso Yamma Babangida Husseini, Majalisa ta riga ta kebe rananr da za ta tantance wadanda aka kawo sunayen nasu har sai ta kamalla aikin tantance mutanen duka, kafin ta fara hutun ta na makonni 6. Babangida ya ce akwai alamun Majalisar dattawa za ta dawo ta cigaba da aikin duba Kasafin kudi da ake sa ran shugaban kasa zai kawo wa Majalisar kafin karshen wannan shekara,
Ya zuwa yanzu dai mutane 28 Majalisar dattawa ta riga ta kamalla tantance su kafin a cigaba da sauran mutane 19 da shugaba Bola Tinubu ya mika masu.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5