Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci Babar Antoni Janar ta kasar da ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da sakin yaran da 'yan sanda suka tsare su bisa zargin shiga zanga-zangar da aka yi a watannin baya.
Kazalika Tinubu ya umarci Ma’aikatar Harkokin Jinkai da ta tabbatar da mayar da wadannan yara gida cikin aminci zuwa ga iyalansu kamar yadda Kakakinsa Bayo Onanuga ya fada a shafin X ranar Litinin.
An gurfanar da mutaum 76, ciki har da yara kanana 30 a gaban kuliya a karshen makon da ya gabata, bisa tuhumar cin amanar kasa da kuma tunzura juyin mulki bayan sun shiga cikin zanga-zangar tsadar rayuwa a watan Agusta da ta yi sanadin mutuwar wasu.
A karshen makon da ya gabata hotunan yaran suka karade shafukan sada zumunta cikin mawuyacin hali, lamarin da ya janyo kakkausar suka daga sassan Najeriya.
Masu zanga-zangar sun gudanar da taruka a Abuja, babban birnin Najeriya, da kuma Legas, babban birnin kasuwanci, da wasu birane don nuna rashin amincewa da sauye-sauyen tattalin arziki da suka jawo hauhawar farashi da kuma karin matsin rayuwa ga talakawan Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin ci gaba da aiwatar da wadannan sauye-sauyen da ya ce suna da muhimmanci domin ci gaba da ceto kasar.