Shugaba Bola Tinubu ya bukaci kafafen yada labarai su goyawa gwamnatinsa baya akan shirinsa na gyaran dokar haraji, inda yace tana da matukar mahimmanci wajen bunkasa tattalin arzikin kasa tare da tabbatar da wanzuwarsa a tsakanin ‘yan Najeriya.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin taron karrama kafafen yada labaran Najeriya (NMMA) da suka yi fice na bana da yammacin Lahadin da ta gabata a cibiyar Muson dake Legas, ta bakin ministansa na yada labarai da wayar da kan jama’a, Muhammad Idris.
Shugaba Tinubu ya ce duk da cewa ra’ayoyi na iya bambanta dangane da bayanan shirin gyaran dokar haraji, sai dai an yi ittifaki game da bukatar yiwa tsarin harajin da ake amfani da shi garanbawul.
Ya kuma bayyana fatan cewa ta hanyar ci gaba da muhawarar da ake yi game da gyaran dokar harajin, za a samu wurare da dama da ra’ayi zai zo daya.
Shugaban kasar ya kara da cewa manufar kudurorin neman gyaran dokar harajin da ke gaban majalisar dokokin Najeriya ita ce daidaita adadin harajin da rage wa talakawan kasar nauyi da kara kason harajin da jihohi za su rika samu da kuma bunkasa harkokin kasuwanci ta hanyar samar da tallafi.
A cewar Shugaba Tinubu, baya ga karin kudaden shigar da ake karba tare da rarrabawa duk wata, akwai kuma hobbasar da aka yi ta tabbatar da ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi wajen sarrafa kudadensu, kasancewarsu gabar gwamnatin da ta fi kusa da jama’a.