Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Macen Farko Mai Tuka Jirgin Sama A Rundunar Sojin Ruwan Najeriya


Changfe Maigari
Changfe Maigari

Wata matashiya 'yar shekaru talatin da uku, mai suna Changfe Maigari, ta kasance mace ta farko da ta zama mai tuka jirgin sama, a rundunar sojin ruwa ta Najeriya, tun kafa rundunar shekaru sittin da suka gabata.

A makon jiya ne, rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta karrama Changfe Maigari da lambar girmamawa da bata lasisin tukin jirgin ruwa, bayan ta sami horo a kasar Amurka.

Changfe Maigari wadda mijinta shima sojan sama ne a Najeriya, ta yi girma a barikin soja ne da ke Kaduna, ta kuma sami horo a cibiyar horon sojoji dake Kaduna, wato NDA, kasancewar mahaifinta shima sojan sama ne, kafin rasuwarsa.

Mahaifiyar Changfe, wacce malama ce a cibiyar fasaha ta mayakan sama dake Kaduna, Nanna Lord-Mallam, ta ce tun tashinta, Changfe ta nuna sha'awar shiga aikin soja.

Changfe Maigari wacce yar asalin jihar Filato ce, daga karamar hukumar Langtang ta Arewa, tana ta samun sakonnin taya murna daga gwamnati da manyan masu fada aji daga jihar.

Tsohuwar 'yar majalisar tarayya daga jihar Filato, Beni Lar tace al'ummarsu na matukar fahariya da wannan fice da diyarsu ta yi.

Lasisin da Changfe Maigari ta samu ya bata damar tukin jirgin sama na soja da na farar hula a ko'ina.

Saurari cikakken rahoton:

An Sami Macen Farko Mai Tuka Jirgin Ruwa A Rundunar Sojojin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG