Amurka ta dagawa Tik Tok kafa don masu amfani da manhajar su ci gaba Da amfani da ita jiya Lahadi, ‘yan sa’o’I bayan da manhajjar watsa hotuna da bidiyon ta daina aiki a matsayin martini ga haramcin da gwmantin tarayya ta Sanya mata, wanda zababen shugaba Donald Trump y ace za iyi kokarin jinkirta dokar haramcin a ranar farko da zai kama aiki.
Trump ya ce yana Shirin fitar da wata dokar da zata baiwa kamfanin Tik Tok da shalkwatar ta take China damar neman wani wanda Amurka ta amince da shi za zai saye kamfanin Tik Tok kafin dokar haramcin ta fara aiki gadan gadan.
Ya bayyana wannan matsayar dake da dangantaka da manhajar shi ta Truth Social, yayin da miliyoyin Amurkawa masu amfani da mahhajar suka wayi gari adireshin su na Tiki Tok sun daina aiki.