TCN Ya Fara Aikin Gyara Lantarkin Arewacin Najeriya

Wutar lantarki ta katse a duk fadin kasar Najeriya

Katsewar layin lantarki ya jefa yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma da wasu sassa na arewa maso tsakiyar Najeriya cikin duhu.

Kamfanin samar da hasken lantarki na Najeriya (TCN) ya fara aikin gyara layin Ugwuaji zuwa Apir mai karfin kilovolt 330 da ya lalace.

A cewar TCN, ya gano matsalar ne da misalin karfe 5 na yamma jiya a yankin Igumale na jihar Benuwe.

TCN ya ce an gano cewa wurin da aka samu matsalar, da tsawonsa ya kai tsakanin falwaya da ‘yar uwarta, wayoyin layin lantarki mai karfin kilovolt 330 ne suka katse a cikin dajin Igumale mai yanayin fadama.

“Sakamakon gano inda matsalar take da yammacin yau, shirye-shirye sun yi nisa ta kai kayan aiki zuwa yankin da al’amarin ya faru domin fara aikin gyara,” a cewar TCN da yammacin jiya Laraba.

Katsewar layin lantarki ya jefa yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma da wasu sassa na arewa maso tsakiyar Najeriya cikin duhu.

TCN ya kara da cewa, duk kokarin tawagar injiniyoyinsu ta gano inda matsalar take bai yi nasara ba har sai da yammacin jiya Laraba.