Tawagar Robert Mueller Akan Binciken Rasha Basu Ji Dadin Takaitaccen Rahoton Atoni Barr Ba

Shugaban kwamitin shari’a na majalisar wakilan Amurka na bukatar Atoni-Janar William Barr ya fidda kuma ya gabatar da duk wasu takaitattun bayanan da mukarraban mai bincike na musamman Robert Muller suka shirya.

Dan majalisa Jerry Nadler, na jam’iyyar Democrat ne ya tura wata wasika zuwa ga Atoni Barr bayan rahotannin dake cewa tawagar ma’aikatan Mueller ba su ji dadin takaitaccen bayanin Atonin ba saboda, rahotannin sun ce, binciken Mueller ya gano wasu abubuwa da zasu kawo cikas sosai ga gwamnatin Trump fiye da yadda Barr ya bayyanawa ‘yan majalissar tarayya da sauran jama’a.

A cewar takaitaccen bayanin rahoton mai shafuka 4 da shi Barr ya gabatar akan rahoton binciken Mueller mai shafuka fiye da 300, ya nuna cewa Trump da wadanda suka yi mashi yakin neman zabe basu yi wata mu’amulla da Rasha ba a kokarin taimakawa Trump cin nasara a zaben shugaban kasa na shekarar 2016 da aka yi.