Tawagar Lauyoyin Trump Na Wargajewa Gabanin Shari'ar Sake Tsige Shi

Lauyoyin tsohon shugaban sun kasa cimma matsaya akan dabarar da ta fi dacewa don kare shi a majalisar dattawan kasar.

Yayin da ya rage mako guda da 'yan kwanaki a fara shari’ar tsige shi karo na biyu a majalisar dattawa, da alama tawagar lauyoyin da ke kare tsohon shugaba Donald Trump na cikin yanayin rashin kintsi.

An sa ran wasu manyan lauyoyi 2 daga jihar South Carolina, Butch Bowers da Deborah Barbier, su ne zasu jagoranci tawagar lauyoyin na Trump. Ko da ya ke, kafafen yada labarai sun fada ranar Asabar cewa sun raba hanya.

Bayan haka, wasu lauyoyin guda 3 da aka sami rahoton suna aiki da tsohon shugaban su ma ba sa cikin tawagar lauyoyin na Trump yanzu, a cewar wasu bayanai da gidan talabijin din CNN ya fara badawa.

An samu rahoton cewa Trump da lauyoyinsa basu daidaita ba akan dabarar da ta fi dacewa don shari’ar da za a fara ranar 9 ga watan Fabarairu.

Tsohon shugaba Donald Trump dai na fuskantar zargin tunzura tarzomar da ke da alaka da masu zanga-zangar da suka mamaye ginin majalisar dokokin Amurka ranar 6 ga watan Janairu. Ranar Talata aka shirya zai maida martani akan wadannan zarge-zargen.