Tauraruwa Mai Wutsiya ISON Zata Bakunci Samaniyar Bil Adama
Hoton zahiri na taurarauwa mai wutsiya da aka sa ma suna "COMET ISON" wanda hukumar NASA ta dauka da na'urar hangen nesa ta Hubble dake shawagi a samaniya, ranar 10 Afrilu, 2013. An dauki hoton ISON tun yana gaba da duniyar Mars
Hoton tauraruwa mai wutsiya ta ISON, kamar yadda wani masanin taurari, Nirmal Paul, ya dauki hotonta daga tsibirin Canary Islands ranar 16 Satumba, 2013. (NASA)
Wannan shi ne zanen awun da aka yi na inda tauraruwa mai wutsiya ta ISON zata bi a yayin da ta doshi rana ta duniyar bil Adama. A cikin watan Nuwamba, 2013, tauraruwa mai wutsiya ta ISON zata gitta kimanin kilomita miliyan 1 da dubu 800 daga doron rana.
Hoton zahiri na taurarauwa mai wutsiya da aka sa ma suna "COMET ISON" wanda hukumar NASA ta dauka da na'urar hangen nesa ta Hubble dake shawagi a samaniya, ranar 10 Afrilu, 2013. An dauki hoton ISON tun yana gaba da duniyar Mars
Wannan hoton wata tauraruwa mai wutsiya ce mai suna "COMET HARTLEY 2" wadda wani kumbon Hukumar NASA mai suna EPOXI ya dauka ranar 4 Nuwamba, 2010 lokacin da yaje shigewa ta kusa da tauraruwar a cikin filin sararin subhana.
Tauraruwa mai wutsiya mai suna Tempel 1, wadda aka cilla kumbo ya sauka a kanta. tauraruwa mai wutsiya dai, curin kasa da duwatsu da kankara ce. Idan dutsen ya doshi kusa da rana, sai tururi da kura su rika fita daga jiki. Wannan tururi da kurar sune ake gani na bin irin wannan dutse shi yasa aka sanya masa suna Tauraruwa mai Wutsihya.
Lokacin da Kumbon NASA ya sauka a kan tauraruwa mai wutsiya. Tauraruwa mai wutsiya mai suna Tempel 1, wadda aka cilla kumbo ya sauka a kanta. tauraruwa mai wutsiya dai, curin kasa da duwatsu da kankara ce. Idan dutsen ya doshi kusa da rana, sai tururi da kura su rika fita daga jiki. Wannan tururi da kurar sune ake gani na bin irin wannan dutse shi yasa aka sanya masa suna Tauraruwa mai Wutsihya.
Saukar Kumbon Hukumar NASA kan tauraruwa Mai Wutsiya Tempel 1
Tauraruwa Mai Wutsiya mai suna "Comet McNaught" wadda ta ratasa ta samaniyar bil Adama a shekarar 2010.
tauraruwa mai wutsiya t-da ta fi kowacce suna, wadda kuma daga gareta aka fara gano asali da siffar taurari irinta, watau "Halley's Comet" wadda take kewayowa ta duniyar bil Adama bayan shekaru 76.