Babban wakilin Koriya Ta Arewa a tattaunawar matakin aiwatarwa da Amurka, da su ka yi jiya Asabar a birnin Stockholm, ya ce tattaunawar ta kawo karshe nan da nan.
“Tattaunawar ba ta zo da irin yanayin da mu ka sa rai ba, karshenta dai ta wargaje,” abin da Kim Myong Gil ya fada kenan a harabar Ofishin Jakadancin Koriya Ta Arewa a birnin na Stockholm.
To sai dai, ‘yan sa’o’i bayan nan, mai magana ta yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Morgan Ortagus ya fadi a wata takardar bayani cewa, “Kalaman da su ka gabata na tawagar ‘yan Koriya Ta Arewa, ba su yi kama da maudu’i da kuma yanayin tattaunawar da aka kwashe sa’o’i takwas da rabi ana yi a yau dinnan ba. Tawagar Amurka dai ta gabatar da kwararan ra’ayoyi, kuma ta yi tattaunawa mai kyau da takwararta ta Koriya Ta Arewa.”