Tattalin Arzikin Najeriya: Sharhin Masana Kan Mukalar Sarki Sanusi

Sarkin Kano, Mallam Sanusi Lamido Sanusi

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa muddin Najeriya ba ta dauki matakan daya dace ba, akan harkokin tattalin arziki nan da shekara ta 2050, kasar za ta zama daya daga cikin mafi talauci a duniya.

Sarkin Kano Mai martaba Malam Muhammadu Sanusi II, ya gabatar da wata mukala a Jami’ar Ibadan da ke Jihar Oyo a wajan wani taro, game da matsayin tattalin arzikin Najeriya nan da shekara ta 2050.

Sarkin ya ce, Najeriya za ta kasance shalkwatar masu fama da talauci ta duniya nan da shekaru 31 masu zuwa, muddin hukumomi ba su dauki matakan da suka dace ba.

Sarki Sanusi ya dora kalaman na sa ne bisa alkaluman kididdiga da aka yi game da yanayin tattalin arzikin duniya na yanzu, inda aka yi hasashen cewa, Najeriya da kasar Dimokaradiyyar Congo ne, za su dauki nauyin kashi 40 cikin dari na matalautan duniya.

Sannan Sarkin ya ce wata kididdiga daga Majalisar Dinkin Duniya ta nuna cewa, a cikin wadannan shekaru, kashi 80 cikin 100 na adadin masu fatara a duniya, za su kasance a Nahiyar Afrika ne, kuma rabin su za su kasance ‘yan Najeriya da Dimokaradiyyar Congo, inda Najeriya za ta dauki mafi yawan wannan adadi.

Yanzu haka masu sharhi kan al'amuran yau da kullum a Najeriya na ci gaba da tsokaci akan mukalar ta Sarkin Kano.

Saurari sharhin da Dr. Abbati Bako (masanin tattalin arziki da siyasa a Najeriya) da Alhaji Bashir (mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a Najeirya) suka yi a wannan rahoto da Mahmud Ibrahim Kwari ya hada mana

Your browser doesn’t support HTML5

Tattalin Arzikin Najeriya: Sharhin Masana Kan Mukalar Sarki Sanusi