TASKAR VOA: Matakan Da Suka Kamata Dakarun Najeriya Su Dauka Don Kawo Karshen Hare-Hare Kan Fararen Hula

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce ba ta gamsu cewa sojojin Najeriya za su gudanar da irin bincike na gaskiya ba a game da harin da sojoji suka kai a kauyen Tudun Biri a Kaduna, wanda ya halaka sama da fararen hula 100.