An fara samun bullar cutar a watan Disamba na shekara ta 2019, a birnin Wuhan a dake kasar China.
Bayan barkewar cutar a wasu kasashen, nan da nan Gwamnatoci suka fara kafa dokar ta baci ta hana shiga da fita, tare da rufe ofisoshin gwamnati, kasuwanni, da wuraren aiki, wuraren shakatawa, makarantu, da dai sauransu.
Cutar ta yi tasiri akan matasa matuka, wanda ya shafi salon rayuwar su. Abu na farko da ya fi kuntatawa matasan shine, rashin zirga-zirga.
Na biyu shine, shiga matsin tattalin arziki, saboda dakatar da ayyukan kasuwanci. Sai na uku kuma wanda shine mai matukar mahimmanci shine, rufe makarantu da dakatar ilimi. Rashin tabbas din lokacin da makarantu zasu bude, ya kawo damuwa ga al’umomi da yawa.
Tasirin duk wadannan abubuwan, ya shafi lafiyar kwakwalwa da lafiyar al'umma. Sannan akwai wani sabon salon da aka lura da shi ga matasa shine karuwar ayyukan jima'i da kuma amfani da magungunan nishadi a tsakanin matasa.