Tashoshin Hutawar Direbobin Manyan Motoci Sun Fara Aiki a Najeriya

Tashoshin dakatar manyan motoci sun fara aiki don rage yawan hatsari da ke faruwa a sanadiyyar gajiya da direbobi ke samu a Najeriya.

Hukumar hada-hadar kasuwanci ta jiragen ruwa da ake kira "Shippers Council" ce ta samar da tsarin da hadin guiwar gwamnatoci da 'yan kasuwa.

Wadannan tashoshin dai da za su taimaka wajen rage cunkuson gefen hanya a wasu garuruwa da manyan motoci ke cin zango kafin tafiya irin su Kari a jihar Bauchi, Marabar Jos, Tafa, Gwalam, Isia Langwa da sauran su, wannan tsari ne da kasashen duniya musamman wadanda suka ci gaba su ka dauka don kare rayuka da dukiya.

Karin bayani akan: Shippers Council, DOGUWA, motoci, Mallam Hassan Bello, Nigeria, da Najeriya.

A taro da masu ruwa da tsaki na hanya a Abuja, babban sakataren hukumar kula da hada-hadar kasuwanci ta jiragen ruwa Mallam Hassan Bello, ya nanata yadda taswirar tashoshin za ta kasance ta yadda har za a sami bunkasar tattalin arziki.

Manyan motoci dai har yanzu su ne babbar hanyar hada-hadar kayan masarufi a Najeriya don rashin hade birane da layin dogo, da hakan ke sa motocin masu nauyi murkushe tituna da haifar da ramuka da kan jawo mummunan hatsari.

Haka nan hatta kafa tashoshin sauke hajar teku a kan tudu ko yankunan da ba sa gabar teku na arewa na samun cikas don rashin ingancin layin dogo, don haka sai manyan motoci da a ke kira DOGUWA ke kwana tafiya don kai muhimman kayaiyakin.

Saurari rahoton Nasiru Adamu Elhikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Tashoshin Dakatawar Manyan Motoci Don Hutawa Sun Fara Aiki a Najeriya