To sai dai kuma a wani bangaren, yanzu yan kasuwa na cin karensu babu babbaka sakamakon wannan matsala, inda komi yayi tashin gwauron zabi a kasuwanni.
Matsalar tashin Dalar tayi tsanani a jihar Adamawa da Taraba, inda ta kai akan canza Dala kusan Naira 400 a kudin Najeriya, lamarin da kan shafi harkokin kasuwanci a yanzu kama daga kayayyakin masarufi zuwa kayan more rayuwa.
A cewar wasu mazauna wadannan jihohi sun koka ne kan yadda farashin kayayyaki ke tashi, sai kuma ace Dala ta tashi, ko kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida na tashi wanda basu da wata alaka da Dala.
Tashin Dalar dai ya shafi yan Kasuwa dake shigowa da kayayyaki da ma motoci daga kasashen waje, haka kuma suma mutanen da ke sayan kayan.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5