Kamar yadda alkaluman babban bankin Najeriya wato CBN suka bayyana, hakan na nufin cewa an sami karuwar kashi 1.2 cikin dari, idan aka kwatanta da dala biliyan 34 da miliyan 417 da ake da su a ranar 18 ga watan Maris.
Wannan karuwar ba ta rasa nasaba da tashin farashin gangar danyen mai samfurin Brent a kasuwannin duniya wanda ya ci gaba da kasancewa kan dala 60 kowacce ganga.
Wannan ya zarta hasashen dala 40 na farashin da aka gina kasafin kudin shekarar 2021 a kai da dala 20.
Duk da haka dai masu fashin baki sun bayyana cewa Najeriya na ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki wanda ke saka masu zuba jari cikin fargabar zuba jarinsu a kasar.
Alkaluman kididdigar kamfanin Fitch na baya-bayan nan dai sun yi hasashen cewa kudadden ajiyar ketare na Najeriya za su karu zuwa dala biliyan 42 a shekarar 2021.
A cikin wani rahoto mai taken, "Matsi akan darajar kudaden kasashen nahiyar Afirka, kudu da hamadar Sahara” hukumar kimanta darajar bashi ta duniya ta jingina hasashen kan tsammanin cewa, danyen mai nau’in Brent zai kai dala 53 a kowace ganga, idan aka kwatanta da dala 43 da santi 1 kan kowacce ganga da aka samu a shekarar 2020.
Bugu da kari, hukumar ta yi hasashen cewa babban bankin Najeriya wato CBN zai bar canjin Naira ya ragu a hukumance a cikin shekarar 2021, duk da ingantattun sharuddan kasuwanci da ajiyar kuɗin waje.
A yayin jawabi a taron kwamitin manufofin kudadde da ya gabata, gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa, sabanin rahotannin da ke yaduwa, Najeriya ba ta sauya manufofinta na kula da harkokin banki ba.