Tashar da za’a gina a tsaunin Mambila zata samar da wuta mega watts dubu uku.
A wata kasuwa akan tsaunin Mambila din, a garin Ngoroje jama’a dake hada hadar kasuwanci na fatan tashar zata tabbata saboda wasunsu na cewa tun suna yara suke jin za’a gina tashar. Wai tun a shekarar 1960 suke jin labarin gina tashar.
Ministan ma’aikatar ayyuka, gidaje da makamashi Barrister Babatunde Fashola shi ya sanar da ba da kwangilar kan kudi dalar Amurka biliyan biyar da miliyan dari bakwai da casa’in da biyu, $5’792b. Cikin kudin, kashi goma sha biyar ne kacal gwamnatin Najeriya zata biya, sauran kuma na ‘yan kwangilan ne da suka fito daga China.
Wazirin Mambila Sanata Marafa Bashir Abba ya nuna farin ciki da sabon matakin. Yace akwai alamu za’a yi aikin yanzu saboda ‘yan China sun fara isa wurin suna zagayawa tare da jibge wasu kayan aiki. Shi ma sakataren magoya bayan Buhari na da kwarin gwuiwar aikin zai kai ga gaci.
Injiniya Ahmed Guroje na kungiyar wanzar da zaman lafiya ya bukaci al’ummar yankin su zauna lafiya domin karfafa wa masu kwangilar gwuiwa tare da cin gajiyar aikin.
Ga rahoton Nasir Adamu El-Hikaya da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5