Taron Yaki Da Cutar Kwalara A Bauchi Ya Kayatar

Dr. Musa Mohammed Dambam, shugaban hukumar tsara ayyukan kula da lafiya daga tushe na Jihar Bauchi, yana gabatar da kasida kan cutar kwalara a zauren taron na Bauchi

Jama'a da kwararrun da suka halarci taron da Muryar Amurka ta shirya sun ce sun karu sosai da irin abubuwan da suka ji, suka kuma gani a zauren taron.

Jama'a da sauran wadanda suka halarci taron da Sashen Hausa na Muryar Amurka ya shirya kan yaki da cutar kwalara sun yaba da wannan taron a zaman wanda ya taimaka wajen dada ilmantar da jama'a da su kansu jami'ai da hukumomi.

"Wannan taro dai abu ne da za a iya cewa, kwalliya ta biya kudin sabulu, saboda duk sakonnin da ake son jama'a su ji su fahimta, sun ji din," in ji Umar Abdullahi, jami'in yada labarai na ma'aikatar kiwon lafiya ta Jihar Bauchi. Ya ci gaba da cewa, "abin ya kayatar musamman idan aka yi la'akari da tsarin yin tambayoyi ma jama'a a karshen kowace kasida da kwararru suka gabatar."

Wannan taro dai ya samu halartar mutane masu yawa daga nan Jihar Bauchi da kuma jihohin dake makwabtaka da ita. Kwamishinan kiwon lafiya na Jihar Bauchi, Mohammed Yahaya Jalam, shi ya bude taron a madadin gwamna Isa Yuguda na Jihar Bauchi.