Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Shirin Fara Taron Yaki Da Kwalara Na VOA A Bauchi


Hoto daga taron yaki da cutar maleriya da cututtukan mata da yara kanana da Sashen Hausa ya gudanar a garin Jalingo, Jihar Taraba a watan Janairun 2010
Hoto daga taron yaki da cutar maleriya da cututtukan mata da yara kanana da Sashen Hausa ya gudanar a garin Jalingo, Jihar Taraba a watan Janairun 2010

Kwararru da dubban jama'a sun fara hallara domin taron da Sashen Hausa na Muryar Amurka ya shirya domin yakar cutar kwalara da wasu cututtukan na mata da yara kanana a Zaranda Hotel dake Bauchi

Yau alhamis Sashen Hausa na Muryar Amurka yake shirin gudanar da taron yaki da cutar kwalara da wasu cututtukan dake addbar mata da yara kanana a hotel na Zaranda dake Bauchi a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Za a fara gudanar da wannan taron da karfe 2 na azahar.

Kwararru a fannin kiwon lafiya, cikinsu har da Dr. Musa Mohammed Dambam, shugaban hukumar tsara kula da lafiya tun daga tushe ta Jihar Bauchi, da Dr. Habib Sadauka na kungiyar T-Ship, da kuma Louise Daniel, kwararriya kan cututtuka masu yaduwa, zasu gabatar da kasidu kan wadannan cututtuka.

Haka kuma, kwararrun 'yan wasan kwaikwayo na ban dariya na Hausa Ibrahim Isah Yado (Ibron Kaduna), Mahmud Shashasha, da Umar Sususu da Aisha Motar Kara da wasunsu zasu gabatar da wasanni kan wadannan cututtukan.

Hukumar Tallafawa Kasashe Masu Tasowa ta Amurka, USAID, ita ma ta turo wakilanta da kwararru a fannoni dabam-dabam domin jin wadannan kasidu tare da nazarin hanayoyin da zata iya kara tallafawa.

Jihar Bauchi na daya daga cikin jihohin da annobar cutar kwalara ta fi yi wa illa a wannan shekara.

XS
SM
MD
LG