A Jamhuriyar Nijer ‘yan jarida sun gudanar da wani taro a jiya Talata a birnin Yamai, da nufin tattauna hanyoyin da za su kawo karshen cin zarafin da ake yi wa mutanen da ke fama da matsalar rashin haifuwa musamman mata, wadanda akasari dangin miji ke dora wa laifin zama silar wannan matsala.
‘Yan jarida sama da 100 ne suka amsa gayyatar gidauniyar Guri Vie Meilleur, hadin gwiwa da gidauniyar Merck Foundation, da nufin samun masaniya daga wasu kwararun likitoci game da dalilan da ke haddasa rashin haifuwa, matsalar da yanzu haka ke ci gaba da jefa mata da dama cikin kuncin rayuwa a nahiyar Afrika, sakamakon wulakanci da suke fuskanta daga abokan zama. Uwargidan shugaban kasar Nijer, Hajiya Aichatou Issouhou Mahamadou, ta ce, shigar da ‘yan jarida cikin wannan tafiya mataki ne da zai taimaka a fitar da mutane daga duhun kai.
Misalai na rashin samun kulawar da ta dace daga al’umma a wajen mutanen da ke fama da matsalar rashin haifuwa, ba su da iyaka inji shugabar kungiyar ‘yan jarida masu kula da sha’anin kiwon lafiya, Hajiya Amina Hachimou.
Shugaban hukumar sadarwa ta CSC, Dr Kabirou Sani, wanda ya yi kiran ‘yan jarida su maida hankali wajen ayyukan fadakar da jama’a akan dalilan da ke janyo rashin haifuwa, ya sanar cewa za a ci gaba da yada irin wannan manufa zuwa yankunan karkara.
Tsananin tsanar da matan da ba sa haifuwa ke gani daga jama’a wani abu ne da ke fitar da wasu daga cikin irin wadannan bayin Allah daga hayyacinsu.
Kashi 85 cikin 100 na matan da ke fama da rashin haifuwa a yankin Afrika da ke kudu da Sahara, sun kamu ne da wata cutar da akan iya magancewa kamar yadda jinsin maza bai tsira ba daga wannan al’amari, yayinda lokitoci su ka ce, dalilan da ke kawo wannan matsala na da tarin yawa.
Ga cikakken rahoton Wakilin muryar Amurka a Yamai, Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5