Kasar Jamus ta tara muhimman masu ruwa da tsaki a dadadden yakin basasar Libiya, da zummar kawo karshen katsalandan din sojojin kasashen waje, da karfafa batun tsagaita wuta da kuma sake bullo da wata hanya a siyasance, ta nemo ma wannan kasa ta arewacin Afirka makoma mai kyau.
Shugabar Jamus Angela Merkel, ta gayyaci shugabannin kasashe 12 da MDD da kungiyar EU, da Kungiyar Kasashen Afirka AU da kuma Kungiyar Kasashen Larabawa, zuwa wannan babban taro na yau Lahadi, a birnin Berlin.
Daga cikin Shugabannin kasa da ake kyautata zaton za su hallara, akwai Vladimir Putin na Rasha, Recep Tayyip Erdogon na Turkiyya, Emmanuel Macron na Faransa, Firimiyan Italiya Giuseppe Conte, Firaministan Burtaniya Boris Johnson, da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo da dai sauransu.
Haka zalika, fitattun masu tafka rikici a Libiya din biyu, wato Firaminista Fayez Sarraj da Janar Khalifa Haftar, su ma za su hallara, a cewar Ministan Harkokin Wajen Jamus, Heiko Maas.