Taron Tattauna Harkokin Cinikayya Tsakanin Amurka Da Afirka

Sakataren harkokin wajen Amurka a taron harkar kasuwanci tsakanin Amurka da Afirka

Taron na mayar da hankali ne kan yadda za a hada kai don bunkasa harkokin cinikayya da saka hannun jari da zai ciyar da tattalin arzikin Afirka gaba don a dama da nahiyar a fagen kasuwancin duniya.

Hukumar kula da harkokin cinikayya ta Amurka na jagorantar wani zaman tattaunawa da ‘yan kasuwar nahiyar Afirka.

Taron na gudana ne a gefen babban taron Amurka da shugabannin kasashen nahiyar Afirka da ake yi a Washington D.C.

Wannan taro na gudana ne tare da hadin gwiwar kungiyar ‘yan kauwar Afirka ta USABF.

Taron na mayar da hankali ne kan yadda za a hada kai don bunkasa harkokin cinikayya da saka hannun jari da zai ciyar da tattalin arzikin Afirka gaba don a dama da nahiyar a fagen kasuwancin duniya.

Yayin wannan babban taro, akwai sashe da aka ware don zaman kulla yarjeniyoyi tsakanin ‘yan kasuwar Amurka da takwarorinsu na Afirka da aka wa lakabi da “The Deal Room” – wato “Dakin Kulla Yarjejeniya.”

Wannan daki zai kasance dauke da manema labarai, inda wakilan kasashen nahiyar Afirka da takwarorinsu na Amurka a fagen kasuwancin za su sanar da kulla yarjeniyoyi a tsakaninsu.