Dalili ke nan kasar ta Nijar ta kaddamar da shirin a yayin wani bikin da shugaban kasar Issoufou Mahammadou ya jagoranta.
Shugaban najalisar matasa Aliyu Umaru ya bayyana gamsuwa da yunkurin da yace zai karawa matasa kwarin gwuiwar cigaba da neman na kai ba tare da shiga wata muguwar hanya ba.
Yace matasa dake mutuwa cikin ruwa ko suke tada hankali a yankin Diffa duk rashin aikin yi ke haddasa su. Idan ana kawo masu tallafi ba zasu shiga wani aikin aika aika ba. Yace wannan dama ce suka samu. Ya kamata matasa su tashi su daina takama da 'yanuwa.
A taron a baza kolin kayan noma da kiwo har ma da kayan masana'antu. Madam Bashir Rakiya wacce take cikin matan da suka kafa kamfani ta kawo abinci mai gina jiki domin yaki da tamowa. Suna kwatantawa mata yadda zasu yi anfani da abubuwan dake cikin gida domin ciyar da yaransu ba tare da dogaro da na kasashen waje ba da sau tari suna da tsada.
Ministar cigaban matasa Hajiya Zainabu Elbak Adam ta yaba da shirin saboda zai bunkasa fannonin da mata suka fi mayarda hankali a kai.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5