Sai dai wasu kungiyoyin fafutukar ganin an yi adalci a sha’anin ma’adanan karkashin kasa sun bayyana cewa ba wani sauyin da zai biyo bayan wannan ziyara.
Ziyarar ta shugaban kwamitin AREVA na gudana ne a dai dai lokacin da farashin makamashin uranium, y ayi faduwar da bai taba yin irinta ba a tarihi, saboda haka shugaban ya fara da zagaya mahakar Arlit, dake yankin Agadez, inda ya ce ya tarar da ma’aikata suna gudanar da aiki babu alamar gajiyawa, duk kuwa da matsanancin halin da ake ciki a yau.
Batun farshin Uranium, a kasuwanin duniya na kan gaban da Phillip Varin, ya ce suka tattauna aka a ganawarsa da shugaba Issoufu Muhammadou, abinda ya ce suna da kwarin guiwar zai iya sauyawa ana gaba.
Da yake tofa albarkacin bakinsa akan wannan batu jami’in, masu fafutukar ganin anyi gaskiya a sha’anin albarkatun karkashin kasa Iliyasu Abubakar Shata, a kungiyar Rotab, ya bayana cewa faduwar darajan Uranium wani abune da aka tsara da gangan domin cimma wani buri.
Jamhuriyar Nijar na cikin jerin kasashe uku, fari albarkatun Uranium a Afirka, arzikin da kafanin AREVA, na Faransa, ya shafe shekaru sama da arba’in, yana hakowa.