Taron Shugabannin Kasashe Biyar Rainon Faransa a Niamey

shugabannin kasashen kungiyar Conseil de L'Entente

Shugabannin kasashen Cote d'Ivoire da jamahuriyar Nijer da Benin da Burkina-Faso da Togo su na taron koli a birnin Niamey a karkashin inuwar kungiyar hadin kan su ta Conseil de L'Entente.
Shugbannin kasashen yammacin Afirka biyar rainon Faransa sun fara taron koli a Niamey babban brnin kasar jamahuriyar Nijer a karkashin kungiyar su ta hadin kai wadda ake kira Conseil de L'Entente. Taron kolin mai taken "Jituwa don karfafa zaman lafiya da bunkasar kasashen biyar" masu yawan jama'ar da ya wuce miliyan sittin da takwas wadanda suka hada da Cote d'Ivoire da jamahuriyar Nijer da Benin da Burkina-Faso da kuma Togo. Shugabannin kasashen da ke yin taron kolin su ne Alhassane Ouattara na Cote d'Ivoire, da Mahamadou Issoufou na jamahuriyar Nijer, da Yayi Boni na Benin, da Blaise Compaore na Burkina Faso da kuma Faure Gnassingbe na Togo. Ga rahoton Abdoulaye Mamane Amadou daga birnin Niamey:

Your browser doesn’t support HTML5

Taron kolin kasashe biyar rainon Faransa - 2:29