Limamin limamai na Majami’ar Lutheran, Dakta Namuel Abubakar Babba ne ya furta haka a jawabin bude taron darikar na shekara-shekara na casa’in bana a garin Demsa dake jihar Adamawa.
Da yake magana akan halin da kasa ke ciki, Nemuel Abubakar Babba, ya nuna takaicin sa da yadda jama’a suka zama masu yiwa kasa da shugabanni mummunar fata maimakon nema masu alheri a kullum. Game da abin da ke rarraba kan ‘yan Najeriya, limamin ya ce gurguwar fahimtar da al’umma ke yi wa addini shi ya jefa ta cikin matsalar da ake fama da ita a halin yanzu.
Shima malam Gayus Bello Auta, cikin hudubar da ya gabatarwa mahalarta taron ya yi nasiha kan illolin kwadayin abubuwan sha’awar jiki kana ya fadakar da su bukatar zama masu gafartawa juna cikin kowanne hali wanda ya karanto a cikin Yakub 4:8 na littafi mai tsarki.
Ana saran nada sabon shugaban Majami’ar Letheran, wanda zai gaji Nemuel Abubakar Babba, ranar lahadi a karshen wa’adinsa na hudu na shekaru goma sha shida wanda ya zo daidai da cikar darikar shekara dari biyar da kafa ta a duniya.
Domin karin bayani ga rahoton Sanusi Adamu.
Your browser doesn’t support HTML5