Taron MDD: Shugaban Ghana Ya Yi Tir Da Rashin Adalci A Duniya

Yayin da yake jawabi a zauran babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 74, shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya ce mu damu ke kasashe masu tasowa mune muka san abinda ake nufi da talauci saboda lamarorin da muke tare da su ako da yaushe, kuma hakan na zubar mana da mutunci.

Ya kuma kara da cewa kawar da talauci shi ne abin da ake gwada mizanin kasashenmu da shi, don haka wajibi ne kowace kasa ta tashi haikan ta yi yaki ta kawar da talauci kuma ta samar da arziki ga jama’arta.

Akufo-Addo ya nuna takaicinsa akan faruwar hakan duk da irin arzikin da Allah ya yi wa Nahiyar Afrika, inda ya ce bai kamata mu manta irin albarkatun da duniya ta doga akai ba wajan tafiyar da masana’antu da kera abubuwa wadanda suke daga Afrika amma har yanzu nahiyar Afrika tana cikin talauci.

Ba ina daura laifi akan wasu da basu a Afrika ba ne, da yake mun taro anan ne domin samun mafita ta bai daya don hakane dole na bayyana irin wannan rashin adalci da ake samu wajan yaki da talauci.

Wasu ‘yan asalin kasar Ghana mazauna nan Amurka sun gudanar da wata zanga zanga ta nuna kin jinin gwamnati akan irin yanayin da kasar ta ke ciki, inda suka koka cewa babu ingantaccen ilimi, tsadar man fetur da kuma yawan garkuwa da mutane da dai sauransu.

Amma wasu kuma suna cewa yanzu ne shugaban kasar ta su yake bullowa da manufofi masu inganci musamman su da suke zaune a kasashen waje suna gani a kasa, kuma a fili lamarin yake kamar yadda shugaban kasar ya samar da ilimi kyauta da saura batutuwa.

Saurari cikakken rahoton da Baba Yakubu Makeri ya aiko mana daga birnin New York:

Your browser doesn’t support HTML5

Taron MDD: Shugaban Ghana Ya Yi Tir Da Rashin Adalci A Duniya