Taron Majalisar Zartarwar Najeriya Na Mako Mako

Shugaba Mohammadu Buhari

Majalisar zartarwa ta Najeriya karkashin jagorancin shugaba Mohammadu Buhari tayi taronta na mako, inda ta tattauna kan al'amuran da suka shafi ilimi da gyaran filayen jiragen sama da kuma maganar haraji na kasa da kasa.

Majalisar dai ta tattauna ne kan muhimman batutuwan dake da tasirin gaske akan Najeriya a dai dai lokacin da ake hada hada ta sha'anin farfadowa da tattalin arziki da kuma inganta sha'anin ilimi da ake ganin yana tabarbarewa a Najeriya.

Ministan sufurin sama na Najeriya Hadi Sirika, yace majalisar ta amince da kirkiro sababbin jami'o'i har guda Takwas, domin taimakawa matasan da basu da hali su shiga jami'a. haka kuma Majalisar ta amince har ta saka hannu kan gyara filayen jiragen sama, kasancewar cikin kasafin kudin shekara ta 2016 akwai kudin aikin filayen jiragen. Sai kuma yarjejeniya tsakanin kasar Najeriya da Kenya kan cewa a rika daukar haraji 'daya kan harkar kasuwanci tsakanin kasashen biyu maimakon kowacce kasa ta caji haraji kan kaya daya.

Sai dai kuma wani kwararre akan tattalin arziki Mallam Shu'aibu Idris, na ganin cewa a halin da Najeriya ke ciki ba a kyauta ba a dauki kudi daga Baitulmalin Najeriya a gyara filayen jiragen sama.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Majalisar Zartarwar Najeriya Na Mako Mako - 3'44"