A wani yunkuri na tunkarar matsalolin tsaro, manyan kwamandojin rundunar mayakan saman Najeriya sun hallara a Abuja inda suke tattauna yadda za a tunkari kalubalen.
Da yake bude taron, Babban hafsan hafsoshin rundunar mayakan saman kasar, Air Marshall Sadique Abubakar ya ce duba da yadda tsari da salon yakin ke caccanzawa, to ko suma dole su fito da sabon salon yakin.
Ya ce ba yadda za a kafe kan abu daya musamman ma yaki irin na sama abu ne dake bukatar sassauya, yadda ake gudanar da shi, inko ba haka ba ba za a sami wani ci gaba ba.
Wani masanin tsaro Wing Commander Musa Isa Salman ya ce irin wannan taro abu ne da za a duba daga ina aka fito, ina ake yanzu sannan ina aka dosa.
Yace sai dai akwai bukatar nan gaba a yi irin wannan taro kuma da masu ruwa da tsaki musamman daga yankunan da ake fama da matsalolin tsaro.
A saurari rahoto cikin sauti daga Abuja a Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5