Taron dai na kungiyoyin manoman yankunan karkara na zuwa ne dab da taron Ministocin aikin gona na kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma ECOWAS, dake da hedikwata a Abuja.
Kungiyoyin dai sunce ‘yan Afirka na da kyakkyawan yanayin ciyar da kansu abinci da har ma su tura zuwa wasu nahiyoyin. Shugaban kungiyar mai suna Banya Jibo, wanda ya zo daga jamhuriyar Nijar, yace akwai bukatar wayarwa mutane kai game da tsarin shigar da abinci tsakanin kasashen kungiyar ECOWAS ta yadda zasu fahimta.
Barista Bello Tukur na kungiyar makiyaya, yayi bayanin taron karfafawa mata gwiwa don noma da sukayi a tsaunin da yafi kowanne tsawo a Afirka, Kilimanjaro dake Tanzania. Bello yace akwai kungiyoyi kimanin guda biyar da suka kai Najeriya, da kuma jaddawa gwamnatoci da su taimakawa mata dake karkara shan wahalar yadda abubuwa ke tafiya.
Taron dai zai gabatar da rahoto ga hedikwatar ECOWAS don yadawa a ayyukan raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-HIkaya.
Your browser doesn’t support HTML5