A yau ne shugabannin kasashen duniya dama suke kwamba a birnin Istambul na kasar Turkiyya don soma taron kolin nan da aka dade ana jira a yi don shimfida ingantattun hanyoyin tunkarar matsaloli masu alaka da al’amarin gudun hijira.
WASHINGTON, DC —
Wannan taron da aka soma a yau kuma za’a ci gaba da yinsa har zuwa Jumu’a, ana fatar zai fito da matakan da za’abi wajen shawo kan bala’ukkan dake yawan faruwa har suna haifarda gudun hijiran milyoyin mutane, sannan kuma da yadda za’a kare kasashe masu tasowa daga irin wadanan fitinnun.
Shugabannin kasashe fiyeda 125 ke halartar wannan taron a kasar ta Turkiyya wacce ita kanta ke cikin jin jiki sosai a sanadin matsalar dubban ‘yan gudun hijiran dake kwarara zuwa cikin Nahiyar Turai.