Muryar Amurka ta zanta da Kyaftin Abdullahi Bakoji Adamu, inda Muhmudu Lalo ya tambeyeshi yadda yake ganin wannan taro da akayi. Ya kuma bayyana cewa abinda yake gani tunda gwamanti ita ke jagorantar komai na al’amarin al’umma, kasancewar ba’a dauki abin da gaske ba a baya to amma canji da aka samu wanda ana tsammanin zai yi tasiri, saboda shugabancin yanzu yana tare da al’umma kuma yana yaki da su masu tayar da kayar baya.
A baya Kyaftin Abdullahi ya fadi cewar irin wannan taron da akayi bazai yi wani tasiri ba, ya kuma bayar da dalilinsa cewa idan da anyi niyyar yakar su to Najeriya kadai zata iya, batare da ta nemi hadin kan kasashen makwabta ba, a dalilin ra’ayin gwamnati wancan lokaci shine makasudin rashin nasara.
Kasancewar makaman da masu tayar da kayar baya ke samu na zuwa ne ta kasashen makwabta Kamaru da Chadi, hadin kan wadannan kasashen zai taimaka wajen dakile makamai da taimako da kungiyar Boko Haram ke samu.
Your browser doesn’t support HTML5