WASHINGTON D.C. —
Cikin jawabin da yayi lokacin da yake bude taron kasa shugaba Jonathan yace kafin wakilan su amince da wani kuduri ko daftari sai kashi saba'in da biyar cikin dari na duk wakilan sun amince, lamarin da ya jawo cecekuce har da tayar da jijiyoyin wuya tsakanin wakilan.
Domin warware takaddamar da ta taso kan abun da shugaban kasa ya fada, shugaban taron kasa Justice Idris Kutigi ya kafa wani kwamiti mai mutane hamsin su taimaka wurin lalubo zaren warware rashin daidaitawar.
Kwamitin ya tsayar cewa kashi saba'in cikin dari na duk wakilan sai sun amince da wani kuduri ko daftari kafin a tsayar da shi a matsayin karbabbe. Shawarar ta yiwa 'yan arewa dadi domin suna ganin basu da rinjaye a taron.
Batun da ya fi daukan hankali shi ne na bin tsarin tarayyar kasa ko fadiraliya inda larduna ko yankuna zasu raba arzikin yankinsu su kuma bi dokokinsu yayin da gwamnatin tarayya zata zama mahada ko lemar gamayya.Shi kwa Ganiyu Adams na kungiyar yarbawa tsantsa yana ganin wasu kudurorin ba zaus samu karbuwa ba a majalisun tarayya tunda su ba sa bin tsarin fadiraliya. Shi ma Chief Samson Abaru daga jihar Rivers cewa yayi da zarar wasu sun ji fadiraliya fushi zasu yi domin a ganinsa fadiraliya ba wai jan ragamar arziki ba ne a'a mallakarsa ne gaba daya.
Sai dai shugaban karamar jam'iyyar Accord Muhammed Na Lado na ganin an kaucewa manufar taron gaba daya. Yace wasu suna labewa da jawabin shugaban kasa su cusa nasu ra'ayin ko abun da suka shirya tun daga gidajensu. Idan ba'a yi hankali ba suna iya kawo matsala nan gaba.
Wani babban lauya Ahamba yace ba rubuta wasu sabbin dokoki kasar ke bukata ba.A'a dokokin ne ba'a bi. Kasar bata bukatar karin dokoki illa yadda za'a bi wadanda akwai yanzu. Kafin taron ya tashi sai da wani sarkin kasar yarbawa ya nemi a basu matsayi a shirin gudanar da mulkin kasar.
Ga rahoto

Your browser doesn’t support HTML5