Taron Kasa da 'Yan Majalisun Najeriya

Fuskokin wasu da zasu halarci taron kasa

Har yanzu ana cecekuce kan taron kasa da za'a yi kwanan nan. Wasu na ganin 'yan majalisun kasar ne ke da hurumin yin hakan yayin da wasu kuma suna cewa kirawo 'yan kasa su yi taron na kan ka'ida.

A ganin Abdullahi Muhammed Inuwa lauya mai zaman kanshi taron wani koma baya ne ga harkokin dimokradiya a Najeriya. 'Yan majalisa sun ci amanar kansu da na kasar domin su ne ke da hurumin yin taron bisa ga kundun tsarin mulkin kasar. Lamarin tamkar wani nuni ne cewa 'yan majalisun basu san kan aikinsu ba kuma basu san abun da suke yi ba. Sashi na biyar na kundun tsarin mulkin Najeriya 'yan majalisu ne kadai zasu yi dokoki kuma suna iya kiran taron kasa. Babu wani kuma hatta shugaban kasa dake da hurumin shirya wani taron kasa. Mai sharhin ya kara da cewa idan 'yan majalisa ba zasu iya yin aikinsu ba to su yi murabus su bar wadanda zasu halarci taron kasa su yi aikinsu. Taron ya nuna gazawar majalisun ne.

Lauya Inuwa yace sun rubutawa 'yan majalisu da shugaban kasa su dakatar da taron. Idan basu yi ba zai garzaya kotu neman a hana taron domin ya kaucewa kundun tsarin mulkin kasar.

Shi ma Farfasa Ango Abdullahi na dattawan arewa na cikin wadanda basu amince da a yi taron ba. Ya sake jaddadawa talakawan arewa cewa su sa ido kan taron domin a ganisa ba zai haifi da mai ido ba. Yace basa musu da kawo 'yan kasa jefi jefi su tattauna kan abubuwan da suka damesu amma watanni shida da suka wuce shugaban da bakinsa yace babu anfanin taron kasa domin akwai majalisu da aka zaba su tattauna matsalolin kasar su kuma yi dokoki. Tambaya nan ita ce menene ya kawo canjin za'ayin shugaban? Yace ba wani abu ba ne illa matsi na siyasa da na kabilanci.

Saidai wani jigo a jam'iyyar PDP Danlami Danfulani yace su kam sun amince da taron domin yana bisa ka'ida.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Kasa da 'Yan Majalisun Najeriya-3' 35"