WASHINGTON, DC —
Shugaban jam'iyyar SDP ya yi watsi da jam'iyyun APC da PDP wadanda yake gani manufofinsu daya ne haka kuma halayensu.
Chief Olu Falae wanda wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya ya zanta da shi yace yadda mutane ke fita daga PDP zuwa APC ko kuma daga APC zuwa PDP ya nuna cewa jam'iyyun biyu basu da akida. Yace yau sai su bar PDP su koma APC. Gobe da safe kuma su koma PDP. Basa la'akari da manufofin jam'yya sai dai su yi kokarin cin zabe ko ta halin kaka.
Chief Falae yana Abuja ne domin yin taron jam'iyyarsa ta SDP da yake jagoranta. Ita dai jam'iyyar ta samo asali ne tun lokacin da marigayi MKO Abiola da Baba Gana Kingibe suka tsaya zabe a karkashin tutar jam'iyyar a shekarar 1992 da aka yi ikirarin sun lashe amma gwamnatin tarayya ta hanasu kama madafin iko.
Da yake cigaba da zargin jam'iyyu biyu Chief Olu Falae yace jam'iyyar PDP ta tsiyata Najeriya. Yace sun tsaya ne su tabbatar da kankamar dimokradiya domin a taimakawa talaka amma ba karawa mai karfi karfi ba a tsarin shugabancin kashin dankalida kasar ke ciki yanzu.
A taron APC wakilin namu ya ci karo da Sanata Haruna Goje tsohon gwamnan jihar Gombe wanda ya yi mulkin jihar na shekara takwas a karkahin jam'iyyar PDP amma yanzu ya canza sheka zuwa APC. To saidai ana raderadin zai koma inda ya fito tambayar da kuma wakilinmu ya yi masa. Sai ya ce shi "bana magana biyu kuma bana yaudara. Tun da nace na bar PDP na koma APC to ai ba zan yi amai in sake lashe aman ba" Yace ba zai rinjayi jama'a su koma APC ba ya kuma barsu ya koma PDP. Yin hakan tamkar bashi da dattaku ke nan.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya