Kwararru a fannin shari’a a Najeriya, sun fara daukar matakan yin garambawul da nufin inganta harkokin Shari’a, a Najeriya, wanda shi ya kawo wasu daga Najeriya, halartar wani taron karawa juna sani a Amurka.
Wani babban Lauya a Najeriya, Barrister Garba Pwul, wanda yake daya daga cikin mahalarta taron yace taron ya hada da alkalai,lauyoyi dakuma ma’akatan shari’a.
A cewar Barrister, Garba Pwul, wannan taron na karawa juna sani zai taimaka gaya wajen yiwa wadanda ake kara adalci, ta inda za’a iya samun mai shiga tsakanin mai kara da wanda ake kara domin samun sulhu batare.
Yace daukar irin wannan mataki zai sa a samu ragowar cinkoso a kotunan Najeriya, ta inda za’a samu yanke hukuncin akan lokaci ba ‘a bar shari’a har sekaru goma ko fiye ana Shari’a daya ba.
Your browser doesn’t support HTML5