Wakilin shugaban kasar Amurka na musamman wanda ya bude taron fadakar da 'yan jarida da masu ruwa da tsaki kafin su kebe dakin taron da ba'a bar 'yan jarida shiga ba ya bada wasu bayanai.
Inji wakilin gidauniyar da kasarsa ta kafa ta tara miliyoyin dala kuma ta amince ta yi anfani da kudaden wajen sake gina birnin Raaqa da wasu wuraren da aka kwato daga ISIS cikin kasar Syria.
Yin anfani da kudin gidauniyar zai ba kasar Syria daman yin anfani da wasu miliyoyin dala wajen sake gina abubuwan jin dadin jama'arta, da hanyoyi da asibitoci da dai sauransu.
Dangane da kasar Iraq kuma wakilin yace suna kokarin kirkiro da yadda zasu sake gina birnin Mosul da wasu wuraren da ISIS ta mamaye ta kuma lalatasu. Zasu yi hakan ne ta hanyar da tafi dacewa da bukatun kasar ta Iraq.
Yace gamawa da kungiyar ISIS gaba daya na bukatar hadin kan duniya gaba dayanta kana daga karshe ya marabci kasashen Chadi da Nijar da Djibuti da yanzu suka hada kai dasu a wannan yaki da ISIS.
Shi ma wakilin kasar Iraq yayinda yake jawabi yace shekaru uku da suka gabata duniya tayi tunanen cewa kasar Iraq ta ruguje gaba daya. Ba zata sake zama kasa ba a duniyan nan tamu. Amma su 'yan kasar suka ce a'a. Hakan ba zai yiwu ba idan aka yi la'akari da cewa Iraq ta yi fiye da shekaru dubu biyar a doron duniya.
Yace gaskiya ne ISIS ta kwace garuruwa da dama amma yau duk an kwatosu saboda haka kamata yayi duniya ta tayasu murnar wannan gagarumar nasara da suka samu.
Ga takaitaccen fasarar abun da aka fada daturanci.
Your browser doesn’t support HTML5