Taron G-8 zai tabo batun samar da abinci a Afirka

Shugaban Amurka Barack Obama

Taron Kolin kasashe takwas masu arzikin masana’antu na (G8), ya shirya sanya batun karfafa samar da abinchi a nahiyar Afirka

Taron Kolin kasashe takwas masu arzikin masana’antu na (G8), ya shirya sanya batun karfafa samar da abinchi a nahiyar Afirka kan ajandar zaman taron da za’a yi a nan Amurka.

Shugaban Amurka Barack Obama, shi ya bada shawarar saka batun kan ajandar taron a matsayinsa na shugaban kasar dake daukan nauyin zaman taron kolin na G8. Matsalar fari na yawaita janyo rashin isassehn kayan abinchi a nahiyar Afirka duk da agajin miliyoyin Dalolin da ake turawa Afirka kowaced shekara.

Kasashen kudu maso gabashin Afirka sun fi fuskanta kamfar ruwa a shekarar da ta gabata, sai mkuma Somalia inda a yanzu ake fama da rashin kayan abinchi. Kazalika akwai wasu kasashen dake fama da wannan matsalar a yankin Yammacin Afirka.