Shugaba Barack Obama na Amurka zai mayarda hankali yau jumma’a a kan batun tabbatar da wadatar abinci a nahiyar Afirka, yayin da zai sake tado da wannan batu a taron kolin manyan kasashe masu arzikin masana’antu da za a yi karshen makon nan.
An shirya shugaban na Amurka zai yi jawabi ga shugabannin Afirka a wurin wani taron koli kan wadatar abinci a yau jumma’a.
Wannan sabon shirin da za a kaddamar yau jumma’a zai yi kokarin kaiwa ga mutane miliyan 50 wadanda ba su da wadatar abinci ta hanyar bunkasa zuba jari a ayyukan noma. A kasashen bakar fata na Afirka, har yanzu kananan manoma ne suke samar da kusan kashi 80 cikin 100 na abinci.
Har ila yau za a tado da wannan batu na samun wadatar abinci a taron kolin kasashen G8, watau kasashe 8 da suka fi arzikin masana’antu a duniya, wanda za a yi kusa da nan Washington.
Shugaba Obama ya gayyaci shugaba Boni Yaya na Jamhuriyar Benin, da firayim minista Meles Zenawi na Habasha, da shugaba John Atta Mills na Ghana da kuma shugaba Jakaya Kikwete na tanzaniya domin su halarci wannan taron koli na kungiyar G-8 da za a yi a gandun shakatawar shugaba na Camp David.
Mataimakin sakatariyar harkokin wajen Amurka mai kula da al’amuran nahiyar Afirka, Johnnie Carson, yace shugaba Obama ya kuduri aniyar janyo hankalin duniya ga irin matsaloli da kuma babbar damar da ake da ita a fannin noma a nahiyar Afirka ta hanyar yin aiki da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar G-8.
Carson ya ce, "Akwai dama mai yawan gaske da kuma yanayin bunkasa noma a Afirka, kuma babu wani dalili ko miskala zarratin da zai sa a fuskanci karancin abinci a nahiyar. Dalilin me zai sa a samu karancin abinci a wannan nahiya wadda a zahiri ma tana iya zamowa babbar mai samar da abinci, ba ma ga Afirka kawai ba, har ma ga wasu kasashen duniya?"
Wani sabon rahoto na Majalisar Dinkin Duniya yace har yanzu kasashen bakar fata na Afirka sune suka fi fama da rashin wadatar abinci, duk da bunkasar da tattalin arzikin yankin keyi gadan-gadan da kuma wadatattun filayen noma da yanayi mai kyau.