Taron dai ya samu wakilcin kamfanonin gida dana ketare, kasancewar Najeriya ta kasance kasa mai fuskantar matsalar samar da hasken wutar lantarki wanda ke haifar da cikas wajen bunkasa masana’antu.
Ma’aikatar samar da wutar lantarki ta nahiyar Afirka mai suna West African Power Industry Convention, itace ta shirya taron da nufin gano bakin zaren warware matsalar hasken wutar lantarki a Najeriya da sauran kasashen Yammacin Afirka.
Kamfanoni masu yawa da suka fito daga kasashen nahiyar Turai da Indiya da China sunyi bajakolin na’urori daban daban na samar da wutar lantarki a kasa da kuma masana’antu, abin da wasu ke ganin yakamata Najeria ta mallaki irin na’urorin na zamani don samar da hasken wutar lankarki ingantacce.
Jami’in yada labarai na hukumar samar da wutar lantarki shiyyar jihar Kano, yayiwa wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin karin haske game da makasudin taron. Inda yace sun halarci taron ne domin su zauna da kungiyoyin da zasu tattauna kan yadda za a inganta hasken wutar lantarki a Najeriya.
Yanzu haka dai yawancin kasashen duniya sun mayar da hankali ne wajen amfani da hanyoyin da basa gurbata muhalli, abin da wasu daga cikin kamfanonin dake halartar taron sukayi bajakolin na’urorin.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5