Taron Addu'o'in George Floyd Ya Tattara Fitattun Mutane a Amurka

Masu jimamin mutuwar George Floyd ba'amurken nan dan asalin Afirka da ya mutu bayan da wani dan sanda farar fata ya danne yuwansa da gwiwa duk da ya yi ta magiyar cewa ba ya iya numfashi, sun hallara a ranar Alhamis a birnin Minneapolis, a tarukan farko da za a yi na nuna alhinin mutuwarsa.

Mutuwar Floyd wacce ita ce ta baya-bayan nan da ta auku cikin jerin mace-macen da ke faruwa tsakanin Amurkawa bakar fata da ‘yan sanda farar fata ke sanadi, ta sa an kwashe sama da mako guda ana zanga zanga a duk fadin Amurka, inda jama’a suka fito suna neman a yi adalci a kuma samar da sauye-sauye.

Shugaban masu fafutukar tabbatar da hakkin al’umma, Rev. Al Sharpton ne ya jagoranci wani kebabben taron addu’o’i wanda ya tattaro iyalai da abokan mamacin wanda ya gudana a farfajiyar jami'ar North Central University, inda aka kayata akwatin Floyd da furanni da kuma hotonsa a gefe.

Sa’o’i gabanin taron addu’o’in, Rev Al Sharpton ya wallafa a shafin sada zumunta cewa, “muna masu tunawa da dumbin mutanen da jami’an tsaro suka kashe ba tare da hakkinsu ba.”

Daga cikin fitattun mutanen da suka halarci zaman addu’o’in na jiya Alhamis a birnin na Minneapolis, akwai Rev. Jesse Jackson, Sanata Amy Klobuchar ta jihar Minnesota da ‘yan majalisar dokokin Amurka da dama.

Baya ga su, akwai fitattun mawaka irinsu Ludacris da jaruman Hollywood irinsu Kevin Hart, Tiffany haddish da kuma T.I.