Taron Addu'o'i Ga Wadanda Suka Rasa Rayukansu a Rikicin Jos

Taron Addu'o'i A Garin Jos

An yi kira ga matasa da su nemi sana’ar yi, don inganta rayuwarsu da ta al’ummarsu.

Taron Addu'o'i A Garin Jos

Tsohon Karamin Ministan Sadarwa a Najeriya, Ibrahim Dasuki Nakande, shi ya yi wannan jan hankali ga matasan yayin gudanar da addu’o'i na musamman ga wadanda suka rasa rayukansu a rikicin da aka yi a garin Jos, a shekarar 2008.

Addu'o'in wadanda aka saba gudanarwa a cikin garin Jos a jihar Filato, ko wacce shekara, an yi na wannan shekarar ne a babban masallacin birnin Jos.

Taron Addu'o'i A Garin Jos

Nakande, wanda ya shugabanci taron addu'ar, ya ce addu'o'in na tunawa ne da wadanda hukumomin wancan lokaci suka yi wa kisan gilla, saboda sun fito suna neman adalci ga alummarsu.

Hukumomin da ake zargi, sun musanta hannu wasu kashe-kashe da ake zargin jami'an tsaro sun yi wa al'umar Musulman.

Sheikh Khalid Aliyu, Sakataren Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta kasa, wanda ya gabatar da makala a wurin taron addu’o'in, ya bukaci hadin kai tsakanin al’ummar garin Jos.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Addu'o'i Ga Wadanda Suka Rasa Rayukansu a Rikicin Jos