Tarihin Shugabanin Hukumar Kwallon Kafar Najeriya

A shekarar 1945 aka kafa hukumar kwallon kafar Najeriya da ake kira Nigeria Football Association ko NFF a takaice, kimanin shekaru 75 da suka wuce kenan yayin da kuma aka kirkiro kungiyar kwallon kafar kasar ta farko a shekarar 1949.

Kungiyar kwallon kafar Najeriya ta yi shugabannin 39 tun daga kafa kungiyar zuwa yanzu, ciki har da turawan Ingila guda bakwai, sauran kuma ‘yan Najeriya ne.

A cikin shugabannin da hukumar ta taba yi wadanda ba ‘yan Najeriya ba ne akwai Pa Mulford, Pius Quist Anthony, DH Holley, P. Harvey, N. Miller, Dennis j. Slattery, da kuma RB Allen.

A cikin ‘yan Najeriya da suka shugabanci kungiyar akwai Godfrey Amachree, FA Ogunmuyiwa, Louis Edet May, MS Adawale (mukaddashi), AB Osula (mukaddashi), Francis Giwa-Osagie, Ishola Bajulaiye, Chuba Ikpeazu, da kuma Godfrey Amachree. Sauran sune Kanar Kevin Lawson, Komodo Edwin Kentebbe, Ademola Adeoba (mukaddashi), Birgediya Emmanuel Sotomi, Lahadi Dankaro, kanar Mike Okwechime, Komodo Edwin Kentebbe, Tony Ikazoboh, Yahaya Obakpolor, Chuba Ikpeazu, Efiom Okon a matsayin shugaban wucin-gadi, sai Tony Ikazoboh a karo na biyu.

Akawi Yusuf Ali, Efiom Okon, Amos Adamu, Emeka Omeruah, Abdulmumini Aminu, Kojo Williams, Dominic Oneya, Ibrahim Galadima, Sani Lulu, Aminu Maigari, Amaju Melvin Pinnick wanda kuma shine shugaban hukumar mai ci a yanzu.

A halin yanzu dai hadaddiyar kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da kuma mai horas da ‘yan wasan sun aike da sako na hadaka inda suke bukatar ‘yan Najeriya su bi dokokin hukumar kula da lafiya ta majalisar dinkin duniya da Cibiyar kare yaduwar cututtuka ta Najeriya wato NCDC, akan batun cutar coronavirus.

Saurari karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Tarihin Shugabanin Hukumar Kwallon Kafar Najeriya