Tarayyar Turai Ta Nade Tabarmar Borin Kunya

Wani jami'in 'yansanda yake wuce gungun bakin haure daga Tunisia a Italy.

Bayan da kasashen duniya suka matsawa tarayyar turai lamba akan bakin haure, yanzu ta yadda ta kashe kudi ninkin ba ninkin akan lamuran bakin haure

Kungiyar Tarayyar Turai dake fuskantar matsin lamba ta shawo kan matsalar kwararar bakin haure,yayinda ta amince ta yi ninkin ba-ninki kudin da take kashewa kan ayyukan nema da ceton rayukan mayakan ruwa a tekun Baha Rum.

Shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel ce ta sanar da hakan jiya bayan wani taron kolin gaggawa da kungiyar ta gudanar a birnin Brussels. Banda haka kuma, shugaban kasar Faransa Francois Hollande yace zai nemi Majalisar Dinkin Duniya ta amincewa kungiyar Tarayyar Turai ta lalata kwale-kwalen da masu fasa kyaurin bil’adama ke amfani da su wajen safarar dubban bakin haure daga kasashen Arewacin Afrika zuwa Turai.

An gudanar da taron kolin kasashen Tarayyar Turai ne kwanaki hudu bayand bakin haure kusan 900 dake cikin wani jirgi dake kan hanyarsa zuwa Italiya ya nutse a gabar tekun Libya, lokacin da ya tuntsure. Wannan ne hadarin bakin haure mafi muni da aka samu a kasashen Turai.

Ana kushewa kungiyar kasashen Turan da ta kunshi kasahe 28 kafin wannan taron, sabili da gaza daukar kwararan matakan shawo kan matsalar kwararar bakin haure ta tekun Baha Rum.