Tarayyar Turai Ta Fadada Takunmkumin da Ta Kakabawa Rasha

Shugabannin Tarayyar Turai

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai da suka gudanar da taron koli jiya Alhamis a Brussels sun amince zasu kara wa'adin takunkumi da suka kakabawa Rasha na wasu watanni shida.

Taron na wuni daya ya kai har cikin daren jiya Alhamis, wanda ya kawo karshen shekara mai cike da rudani ga kungiyar mai wakilai 28, yayinda ake ci gaba da ayar tambaya kan makoma da kuma tasirin kungiyar mai kasashe 28.

Batun kara tsawon takunkumi kan Rasha bai zo da mamaki ba.Domin ko a farkon makon nan an ji shugabar Jamus Angerla Merkel da shugaban Faransa Farncois Hollande suna bayyana goyon bayansu kan fadada takunkumin, ganin Rasha ta kasa mutunta yarjejeniyar a aka kulla a Minsk dangane da rikicin da a keyi a Ukraine. Kasashen suna daukar wannan matakin ne duk da matsin lamba daga masu zuba jari a turai ciki harda Jamus na ganin an rage ko janye takunkumin baki daya.

Masu fashin baki suka ce rashin kwarin guiwa na ci gaba da aiki da takunkumin da aka kakabawa Rasha ba zai rasa nasaba da kudurin shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump na aiki kud da kud da Rasha wajen warware matsaloli da kuma yaki da ta'addanci ba.