Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadar Shugaban Amurka Ta Zargi Shugaban Rasha da Kai Harin Dagula Zaben Kasar


 Josh Earnest, kakakin Fadar White House
Josh Earnest, kakakin Fadar White House

Ahalinda ake ciki kuma, fadar White House ta shugaban Amurka, jiya Alhamis tayi nuni da cewa shugaban Rasha Vladimir Putin shi ya bada umarnin a kai hare hare ko kutse ta komputa, domin dagula zaben shugaban Amurka.

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, yana suka ko zargin cewa wannan wani yunkuri ne ko kokarin yi masa zagon kasa, saboda nasarar da ya samu kan Hillary Clinton.

Gwamnatin Obama bata nuna wata shaida kai tsaye kan zargin data yiwa shugaban na Rash aba. Ikirarin da "Moscow ta kira abun dariya kuma shirme kawai".

Kakakin fadar shugaban na Amurka Josh Earnest yayi nuni da bayanai da hukumomin leken asirirn na Amurka suka yi cikin watan Okotoba, cewa "irin wannan kutsen sai manyan jami'an kasar Rasha ne zasu bada irin wannan umarni".

Amma Trump a shafinsa na Twitter yace "idan Rasha ko wata hukuma tana kutse, me yasa Fadar White House ta kasa daukan mataki tun lokacin da suka sani? Me yasa suka fara korafi bayan da Hillary ta sha kaye.

Earnest yayi watsi da duk wata damuwar neman yiwa sabuwar gwamnatin makarkashiya, yana mai cewa shugaba Obama ya fada karara cewa yayi kudurin ganin an mika gwamnati ba tareda wani cikas ba.

XS
SM
MD
LG