Tarar Naira Miliyan 5 Ga Duk Masu Yada Labaran Karya

Alhaji Lai Mohammed Ministan Watsa Labarai Da Al'adu

Ministan watsa labarai da al'adu na Najeriya Alhaji Lai Mohammed, ya shaida cewar mahukuntan kasa sun amince da a sake duba wata tsohuwar doka, da ta bada izinin ci tarar naira miliyan biyar ga duk wata kafa da ta yada labaran kanzon kurege, haddasa kiyayya, rashin jituwa da dai makamantansu.

Ministan ya bayyana haka ne a wata ganawa ta musamman da manema labarai, bayan kaddamar da wani kwamiti karkashin jagorancin Farfesa Armstrong Idachaba, da zai tabbatar da gyare-gyare a hukumar kula da kafofin yada labarai ta kasa, inda ba za a bari siyasa ta shiga harkokin hukumar ba.

Lai Mohammaed ya ce babu gwamnatin da ta san abinda ta ke yi, za ta amince da wannan dabi'un da zasu iya kawo rashin jituwa a tsakanin al'umma, saboda haka gwamnati za ta yaki kowace kafa ce, ko ta wacce hanya da doka ta bada izinin yi.

Matakin dai, yayi ma Ciroman Bakan Daura dadi, inda yayi tsokaci da cewa, Najeriya tana da jami'an tsaro kwararru da za su iya kama duk wanda yayi irin wannan aika-aikar a kafafen yanar gizo.

Ga cikakken rahoto daga wakiliyar muryar Amurka Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Tarar Naira Miliyan 5 Ga Duk Masu Yada Labaran Karya