TARABA: Kungiyar Maharba Ta Kashe Sama Da Mutane 12 a Karamar Hukumar Bali

Maharba

Ana zargin 'yan banga sun kashe mutane sama da goma sha biyu a yankin Kukana zuwa Jatau da ke karamar hukumar Bali, sun kuma kona gidajen sullubawa dake zama a rugar da kuma kore musu garken shanu sama da goma a rugar. 

A hirar shi da Muryar Amurka, Umar Mai Saje Jatau Mai-Anguwar Jatau ya tabbatar da cewa, 'yan bangan sun kashe mutane goma sha biyu nan take a gaban sa kuma suka ce sai sauran sun bar rugar baki daya.

Abubakar Jatau ya ce yanzu haka dai 'yan bangan suna nan cikin daji har sai abinda Allah yayi, kan kawo karshen matsalar rashin tsaron da ya addabi yankin nasu.

A nashi bayanin, Muhammad Juli, daya daga cikin wanda aka kashe mishi 'yan uwansa har biyu tare da dauke musu baburansu ya ce basu ji dadin al'amarin ba amma dai suna bukatar taimakon gwamnatin jiha da na tarayyar Nigeria akan lamarin.

SP Abdullhi Usman kakakin Rundunar 'yan sandar jihar Taraba, ya tabbatar da cewa 'yan bangan da ake zargin, sun ware kansu ne suka tafi yin wannan aikin ba tare da sanin hukumar 'yan sandar jihar Taraban ba, amma dai ya zuwa yanzu basu yi nasarar kamo wadanda ake zargi da yin wannan aika aikar ba a yankin.

Saurari rahoton Salisu Lado cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

ANKASHE MUTANE SHABIYU A JATAU DAKE BALI L G A.mp3