Jihar Taraba dai na cikin jihohin da aka samu tashe tashen hankula lamarin da kan jawo asarar rayuka da dukiya.
Sheikh Bala Lau, wanda yake jihar Taraba a bisa ziyarar aiki da yake yi zuwa jihohin Nijeriya, ya ziyarci gwamnan ne a fadar gwamnatin jihar Taraba, tare da rakiyar manyan malamai irin su; Sheikh Isah Taliyawa, Gombe, Dr. Jalo Jalingo, Sheikh Kabir Gombe, Daraktan Agaji na kasa da Injiniya M.I Sitti, da sauran manyan malamai da shuwagabannin kungiyar.
A yayin da yake jawabi, Sheikh Bala Lau, yace wajibi ne gwamnan ya kasance mai adalci yayin gudanar da mulki. “Mai girma gwamna, bayan mun maka fatan alkhairi, muna kuma jan hankalin ka, muna kuma yi maka nasiha da dukkan ‘yan majalisar ka, shugabanci yana bukatan adalci. Duk wanda zai yi shugabanci, to yana bukatar ya dauki kowa a matsayin nasa.
Shima da yake jawabi, gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku, yayi godiya da ziyarar da kungiyar ta kawo jihar Taraba tare da saba layar cewa shi kullum fatansa shine a samu zaman lafiya a Taraba.
Jihar Taraba dai ta yi fama da tashe tashen hankula dake da nasaba da rikicin addini ko na kabilanci da sau tari kan jawo asarar rayuka da kuma dukiya batun da ake dangantawa da son kan shuwagabanin siyasar jihar.
Alh.Hassan Jika Ardo, tsohon shugaban jam’iyar APC, a jihar kuma daya daga cikin wadanda suka tsallake siradin majalisar dattawa a tantancewar sunayen Ambassada da aka yi kwanakin nan yace dole ‘yan Taraba su kai zuciya nesa.
Ibrahim Abdul’Aziz ya aiko mana da wannan rahoto.
Your browser doesn’t support HTML5