Shugaban hukumar filayen jiragen sama na Najeriya Saleh Dunoma, yace aikin gyaran filin na ci gaba kamar yadda aka tsara yana mai cewa a yanzu haka an tune duk inda ake da bukatar shinfida sabon dabe.
Shugaban ya kara da cewa sun samu tabbaci daga masu aikin cewa za a kammala aiki a cikin wa’adin da aka dauka na gyaran, yana mai cewa idan aka kammala aikin kafin a sake waiwayar gyaran filin zai kai shekaru goma zuwa goma sha biyar.
Yanzu dai fasinjojin jragen sama daga Abuja akan dauke sune cikin motoci zuwa Kaduna inda ‘yan Sanda ke masu rakiya haka ma yake ga masu fitowa daga filin jirgin sama na Kaduna masu zuwa Abuja.
Wasu masu harkar kasuwanci a filin jirgin sama na Abuja sun koka akan rashin hada hada kamar yadda aka saba wanda yasa kudaden da suke samu na shiga ya ragu.
Facebook Forum